Yadda Yemen ta ke yaƙi da cutar korona

An wallafa

BBC ta kasance kafar watsa labarai a duniya ta farko da ta isa Yemen domin ganin yadda ta ke yaƙi da Covid-19 tun bayan ɓarkewar cutar.

Da ma dai ƙasar tana fama da matsananciyar matsalar 'yan gudun hijira sanadin yaƙin da ya ki ƙarewa.

Yemen ta rabu gida biyu inda 'yan Houthi ke zaune a arewaci, yayin da gwamnatin da kasashen duniya suka yarda da ita ta ke da iko a kudancin ƙasar.

Duk da cewa ana fama da annobar korona, amma ɓangarorin biyu ba su daina yaƙi da juna ba.

Ga rahoton da wakilyar BBC ta aiko mana daga babban birnin kasar Sanaa.