Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyo: Koriya Ta Arewa na tallata 'kyakkyawar' manufar ƙasarta a Youtube
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Ana yi wa Koriya Ta Arewa ƙasar da ke cike da sirri wacce ba ta so a san me take ciki a duniya, sannan ƙasashen yamma sun daɗe suna bayyana irin yadda ake take haƙƙin ɗan adam a can.
Wannan wani bidiyo ne da ke nuna yadda wata ma'aikaciyar gidan talbijin na ƙasar ke nuna irin kywau da yadda rayuwa ke tafiya aƙasar ana wallafawa a shafukan sada zumunta.
Sai dai masu sharhi sun ce wataƙila ƙasar na ɓoyewa abubuwa da yawa fiye da bayyana zahiri ga mutane.