Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Shin farfadiya na da alaƙa da shafar aljanu?
A ƙasashen nahiyar Afrika akwai camfe-camfe da dama dangane da farfadiya.
Sau da yawa akan ce ba a zuwa kusa da mai cutar saboda idan aka shafe shi, ana iya ɗauka.
Wani lokaci kuma a ce aljannu ne suka shafi mai fama da cutar.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce ana iya gane farfadiya idan mutum yana yawan yanke jiki ya faɗi, kuma duka jikinsa ko wani bangare na jikin ya rika jijjiga.
Sannan wani lokaci ana samun gushewar hankali da yin fitsari ko bayan gida ba tare da an san an yi ba.
WHO ta ce kusan mutum miliyan 50 ne suke fama da cutar farfaɗiya a fadin duniya, wanda hakan ya sa ta zama ɗaya daga cikin cutar kwakwalwa da suka fi shahara a duniya.
Hukumar ta ce kashi tamanin cikin ɗari na mutanen da ke fama da wannan cuta na zaune ne a ƙasashe masu tasowa.
Me ke janyo wannan cuta? Yaya rarrabuwar cutar ta ke a likitance? Akwai wasu jerin mutane ne da cutar ta fi kamawa?
Dakta Oseghale Joyce, ƙwararriya a bangaren lafiyar ƙwaƙwalwa ta amsa wadanann tambayoyin da ma wasu a shirin na wannan makon.