Hagia Sophia: Bayani kan Cocin da aka mayar Masallaci

An wallafa

Ɗumbin Musulmi ne suka tarodon fara gudanar da Sallar Juma'a karon farko a mashahurin ginin tarihin duniya na Hagia Sophia da ke birnin Santambul.

Matakin na zuwa ne bayan sanarwar da gwamnatin Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ta bayar don mayar da ginin zuwa masallaci a watan jiya.

Tun ainihi dai an gina Hagia Sophia a matsayin cocin daular gabashin Roma ko kuma Byzantine, amma sai aka mayar da shi zuwa masallaci bayan cin birnin Santambul da daular Ottoman ta yi a 1453.

A 1935 ne kuma, mutumin da ya assasa Turkiyyar zamani wadda ba ruwanta da addini, Kemal Ataturk, ya mayar da Hagia Sophia zuwa ginin adana kayan tarihi.