Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda intanet take taimaka min wurin isar da saƙon Allah - Sheikh Nuru Khalid
An wallafa
Fitaccen malamin addinin Musuluncin na da ke Abuja, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya ce intanet ta taimaka masa sosai wajen isar da sakon Allah ga duniya.
A hirarsa da BBC, Sheikh Khalid ya ce tun daga shekarun 1990 yake amfani da intanet wajen gudanar da tafisi da sauran karantarwa, ko da yake a wancan lokacin "intanet tana da wahalar samuwa".