Coronavirus: Kasashe na watsi da kayayyakin China

An wallafa

Gwamnatocin kasashen turai da dama sun yi watsi da kayayyakin da ake kerawa a China domin yaki da annobar coronavirus.

Dubban kayan gwaji da tukunkumin fuska ba su da inganci ko sun lalace, a cewar mahukuntan Spaniya da Turkiya da kuma Netherlands.

Dubban mutane ne ke dauke da kwayar cutar coronavirus a turai.

Sama da mutum dubu 10 sun mutu a Italiya tun bayan bullar cutar a kasar.

A birnin Wuhan na China cutar ta soma barkewa a karshen shekara ta 2019.

Gwamnatin kasar ta dau matakai masu tsauri na hana zirga-zirga domin dakile annobar.

Me ne ne laifin kayayyakin?

A ranar Asabar, ministan lafiyar Netherland ya sanar da cewa ya janye takunkuman fuska dubu 600.

Kayan sun iso kasar ne daga China a ranar 21 ga watan Maris, kuma an raba su a asibiti tsakanin jami'an lafiya.

Jami'ai a Dutch sun ce takunkumin ba shi da inganci, sannan baya aiki yadda ya dace, duk da cewa sun shigo da su a matsayin masu inganci.

Jami'an sun ce ''An dakatar da amfani da sauran kayayyakin cikin hanzari kuma dama ba a rarrabasu ba, kuma yanzu mun yanke hukunci ba zamu yi amfani da kayayyakin ba.''

Gwamnatin Spaniya ita ma ta fuskanci irin wannan matsalar da kayayyakin na gwaji da ta yi oda daga wani kamfanin China.

Ta sanar da cewa ta siyo dubban kayayyakin gwaji domin dakile bazuwar annobar, sai dai daga bisani ta ba da sanarwar cewa na'urar da ta siyo kusan dubu 60 ta gaza tantance ko mutum na dauke da cutar.

Ofishin jakadancin Spaniya da ke China ya wallafa cewa kamfani da ke samar da na'urar, Shenzhen Bioeasy Biotechnology, ba shi da lasisi a hukumance daga mahukuntan lafiyar China na sayar da kayayyakinsa.

Ya kuma bayyana cewa kayayyakin tallafi daga gwamnatin China da Alibaba ba su danganci wadannan kayayyaki na kamfanin Shenzhen Bioeasy ba.

Ita ma Turkiya ta sanar da cewa ta siyo irin wadannan kayayyaki daga China wanda ba sa aiki yadda ya kamata, ko da yake ta ce akwai wasu dubu 350 da ke aiki da kyau.

Wadannan zarge-zarge na rashin ingancin kayayyakin China ya zo ne bayan masu suka sun yi gargadin cewa kasar na iya amfani da barkewar wannan annoba wurin karfafa tasirinta a duniya.

Wanne hali ake ciki a Turai?

A ranar litinin mutum 812 annobar ta hallaka a Spaniya a cikin sa'o'i 24 - wannan ya kawo adadin alkaluman mamata zuwa 7,340. Akwai kuma sama da mutum 85,000 da ke dauke da cutar - adadin da ya zarta na China.

An dau sabbin matakai a Spaniya da suka danganci haramta fita aiki na mako akalla biyu.

Har yanzu dai Italiya ce kasar da cutar ta fi yiwa illa a duniya.

Sama da mutum dubu 10 ne suka rasa rayukansu, sannan akwai dubu 100 da ke dauke da annobar. Amma dai Amurka ce cibiyar cutar a yanzu inda mutanen da suka harbu da cutar a kasar ya zarta kowacce kasa.