Na gode wa Allah da Buhari bai mayar da ni minista ba – Dalung

An wallafa

Latsa bidiyon da ke sama domin kallon cikakken bidiyon

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni na Najeriya Solomon Dalung, ya shaida wa BBC cewa bai ji bacin ran rashin mayar da shi minista ba.

Mista Dalung ya ce watakila Allah na nufinsa ne da alheri ko kuma ya kare shi da wani sharri ne ta hanyar rashin komawarsa kan mukamin.

Ya ce shi ya yi gwagwarmayar a zabi Shugaba Muhammadu Buhari ne ba wai don kawai ya ba shi mukami a gwamnati ba.

Bidiyo: Abdulbaqi Jari