Gwamnan Gombe ya mayar wa Kayode Fayemi

An wallafa

Latsa wannan hoton domin sauraron gwamna Muhammad Inuwa Yahaya.

Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya ce gwmnan jihar Ekiti, Fayemi Kayode ra'ayinsa kawai ya fadi kan rugujewar jam'iyyar APC.

A kwanakin baya ne dai Kayode Fayemi ya ce idan har jam'iyyar ba ta gyara halinta ba to lallai jam'iyyar za ta ruguje.

Gwamna Muhammad Inuwa ya ce duk da cewa ba zai ce babu matsala a jam'iyyar APC ba, amma yana ganin matsalar ba ta kai girman fasa jam'iyyar ba.