Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sadiq Saleh: Matashi mai muryoyi fiye da 10
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Sadiq Saleh Abubakar mai fassara ne, yana fassara fina-finai musamman na Indiya zuwa harshen Hausa.
Ban da fassara yana iya yin magana da muryoyi daban-daban kamar ta tsoho da yaro da ta mata har ta mai barkwanci.
Ya ce ya samu nasarori da yawa ta wannan harkar. Jami'ar Bayero ta karrama shi don gudunmowarsa a bangaren habaka harsuna da ci gaban harshen Hausa.
Haka zalika, Netflix, babban kamfani da ke dora fina-finai a intanet ya yi magana da Sadiq don ganin yadda za su cimma wata yarjejeniya inda Netflix za su rika ba su kwangila ta harkar fassara fina-finai zuwa harshen Hausa.
Bidiyo: Fatima Othman