Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ban taba amfani da kwakuleta ba' - Yaro mai baiwar lissafi
An wallafa
Ahmed Buhari wani yaro ne mai shekara 17 wanda ya ke da baiwar lissafin da kuma saurin kirge.
A cewar mahaifiyarsa an haife shi ne yana da bukata ta musamman, dan haka yake fama da hardewar harshe.
Samun wannan labari ya sa BBC ta je birnin Lafia na jihar Nasarawa, domin ganin irin baiwar lissafi da Allah ya yi masa.
Da kuma irin saurin da ke gare shi da kwatankwacin irin saurin da ya ke yi wurin amsa tambaya daya ko kuma fiye da haka.