Yadda labaran bogi ke shafar BBC Hausa

An wallafa

Yayin da zabuka ke kara karatowa ana ci gaba da yada labarai na bogi ta yadda wasu suke bude shafukan bogi da sunan wasu manyan kafafen yada labarai.

BBC Hausa ma ba ta tsira ba daga irin wannan al'amari inda wasu ke amfani da sunanta wajen bude shafukan sada zumunta musamman Facebook da Instagram na bogi.

Halima Umar Saleh ta tattauna da Umar Rayyan wanda shi ne mai kula da shafukan sada zumunta na BBC Hausa kan wannan batu.

Sai ku latsa alamar lasifikar da ke jikin hoton da sama don sauraro.