Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Iyayen 'yan Isra'ila da ke hannun Hamas sun yi roko ga al'ummar duniya
Reshen Hamas mai gwagwarmaya da makamai, rundunar al-Qassam ta fitar da wani da ke nuna wata matashiya Ba'isira'iliya 'yar asalin Faransa mai shekara 21, Mia Shem, wadda aka sace ta a wani wurin shagali a Isra'ila.
Ta ce tana daya daga cikin mutanen da aka kama a wurin shagalin kade-kade na Supernova a kudancin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba sannan aka kai su Gaza inda ake garkuwa da su.
Bayan fitar bidiyon ne, iyayen Mia suka gudanar da wani taron manema labarai a Tel Aviv inda ta yi roko a saki yar tata.
Rike da hoton Mia, mahaifiyarta Keren Shem ta ce: “Ina rokon al'ummar duniya ta dawo min yarinta gida."