Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Haɗuran da marasa lafiya ke fuskanta a yayin kulawa
Miliyoyin mutane ne ke fuskantar cutarwa a yayin da ake kula da su a cibiyoyin kiwon lafiya, lamarin da hukumar lafiya ta ce za a iya kauce masa.
Hukumar ta bayyana bai wa marasa lafiya kariya da cewa yanayi ne na rashin duk wani abu da zai iya cutar da su. Haka zalika matuƙar rage duk wani haɗarin da zai kai ga cutar da marasa lafiya ba da niyya ba.
Hanya ta farko da WHO ta ce marasa lafiya na fuskantar cutarwa ita ce, ta wajen bayar da magunguna.
Sai kura-kuran da ake samu a wajen yin tiyata.
Wata matsalar kuma ita ce ta ɗaukar ƙwayoyin cuta, wanda hakan ke janyo daɗewa ana jinya a asibiti da janyo nakasa na dogon lokaci da kuma fuskantar matsalar bijirewa magungunan kashe ƙwayoyin cuta.
Sai dai fiye da kashi 50 cikin ɗari na cutarwar da mara lafiya ɗaya ke fuskanta a cikin kowane mutum 20, abu ne da za a iya kaucewa.
Don haka hukumar ta jaddada muhimmancin bayar da kariya ga marasa lafiya a lokacin da suke samun kulawa a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya.