Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mini Hanya tare da Gwamnan Katsina Dikko Radda
Kimanin makwanni biyu da suka gabata ne gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya kaddamar da rundunar yan sintiri ta jihar wadda ta yi wa lakabi da Community Watch Corp.
Hakan na zuwa ne yayin da jihar, kamar sauran jihohin arewa maso yammacin Najeriya ke fama da matsalar tsaro.
A wata tattaunawa da manema labaru, gwamnan ya ce babu ranar da za ta zo ta wuce ba tare da matsalar tsaron ta haddasa mutuwar wani daga cikin al’ummar jihar ba.
A tattaunawarsa da Rabiatu Kabir Runka lokacin ziyarar da ya kawo ofishinmu da ke Abuja, gwamna Dikko Radda ya yi bayani kan yadda aka samar da rundunar da kuma fayyace wasu abubuwa na siyasa da suka faru tun bayan karbar mulkinsa a jihar.