Gane Mini Hanya tare da Gwamnan Jigawa

Gane Mini Hanya tare da Gwamnan Jigawa
An wallafa

A Najeriya gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi na cikin shugabannin da ba a kai musu wargi.

Ko a `yan kwanakin nan an gan shi a wani hoton bidiyo da aka yi ta yadawa ta intanet yana nuna damuwa game da yadda wasu jami`an gwamnati suka yi rub-da-ciki a kan wasu kudade, har ya yi alawashin cewa ba za ta sabu ba.

A filin Gane Mini Hanya na wannan makon, Ibrahim Isa ya tattauna da shi don jin abin da ya yi zafi, da wasu batutuwa da suka shafi halin da ake ciiki a Najeriya, musamman batun janye tallafin mai.

Amma ya fara ne da tambayar gwamnan abin da ya tarar bayan ya karbi ragamar mulkin jihar Jigawa