Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mini Hanya: Tare da Farouk Adamu Aliyu 19/04/2025
A Najeriya ana ci gaba da tankiya da nuna wa juna yatsa tsakanin mutanen tafiyar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari, bayan wani ɓangare ya fito ya jaddada mubayi'a ga Shugaba Bola Tinubu.
Ƙura ta fara turnuƙewa ne bayan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Elrufai ya fice daga jam'iyyar mai mulki, ga kuma raɗe-raɗin cewa wasu ma na kan hanya, inda suke zargi gwamnatin Tinubu da sauka daga kan ƙa'idojin APC na ainihi.
Sai dai, tsohuwar CPCn tsagin Umar Tanko Almakura na cewa ba da su ba.
A hirarsa da BBC, Hon Faruq Adamu Aliyu, jigo a tafiyar ya ce su zama daram a APC ,kuma ba za su daina goyon bayan Tinubu na.