Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muhimmancin awon ciki ga ciki
Zuwa awo asibiti domin ganin kwararrun ma’aikatan lafiya, na da matukar muhimmanci ga mata masu juna biyu, a cewar likitoci.
Saboda a lokacin awo ne ake duba lafiyar mai ciki da dantayinta, a kuma taimaka musu da shawarwari da magungunan kariya daga wasu cututtuka da ke kaiwa ga mace-macen mata masu juna biyu da kuma jarirai.
Cututtuka kamar na zazzabin cizon sauro da ciwon suga da hawan jini da cutar HIV na daga cikin cututtukan da ke barazana ga rayukan mata masu ciki.
Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta kara yawan lokutan da ya kamata mace mai ciki ta je awo asibiti zuwa takwas mafi karanci.
A baya dai hukumar ta bayar da shawarar cewa, masu ciki za su iya zuwa awon ciki sau hudu mafi karanci.
Wasu alkaluman da asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya ,UNICEF, ya fitar sun nuna cewa, kasashen da ke kudu da hamadar Saharar Afrika da kuma wasu a kudancin Asia su ne koma baya wajen matan da ke zuwa awon ciki.
A cewar asusun, matan da ke samun ganin kwararrun ma’aikatan lafiya a yankin na kudu da saharar Afrika kashi 24 ne cikin dari.
Yayin takwarorinsu da ke kasashen yankin Latin Amurka da Caribbean da kuma nahiyar Turai suka haura kashi 90 cikin dari.