Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muhimman abubuwan da suka faru a duniya cikin shekarar 2023
- Marubuci, Ahmad Bawage
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Hausa
- Aiko rahoto daga, Abuja
- An wallafa
Yayin da 2023 ke bankwana, abubuwa da dama sun faru a shekarar, waɗanda a tarihin kusa-kusan nan da wuya a iya mance su.
Mafi girma daga ciki shi ne ƙazamin yaƙin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin Isra'ila da Hamas, da mummunar girgizar ƙasa a wasu ƙasashe, wadda ta yi sanadin mutuwar ɗaruruwan mutane da sauransu.
Saboda haka, mun waɗannan da kuma ƙarin wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a shekarar.
Girgizar ƙasa a Turkiyya da Syria
A watan Fabrairu ne, wata mummunar girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 7.8 ta auka wa wasu yankunan Turkiyya da Syria, inda ta kashe sama da mutum 7,000.
Alƙaluman da aka fitar a lokacin daga Turkiyya da Syria sun ce fiye da mutum 15,000 ne suka jikkata sakamakon iftila'in girgizar ƙasan.
A 1999, irin wannan mummunar girgizar ƙasar ta yi ajalin mutane sama da 17,000.
Indiya ta zarce China a yawan jama'a
A shekarar ta 2023 ne dai, Indiya ta zarce China a matsayin ƙasa mafi yawan al'umma a duniya.
Ƴawan al'ummar Indiya dai sun kai yawan mutum biliyan ɗaya da miliyan ɗari huɗu da ashirin da biyar da dubu ɗari bakwai da saba'in da biyar da ɗari takwas da hamsin.
An yi hasashen cewa Indiya za at ci gaba da rike wannan matsayi har na tsawon gomman shekaru masu zuwa.
Ƙasashen na nahiyar Asiya ne ke da fiye da kashi ɗaya cikin uku na al'ummar duniya tsawon sama da shekara 70.
Naɗin sarautar Sarki Charles III
A watan Mayun shekarar da muke bankwana da ita ne, aka yi bikin naɗin sarautar Sarki Charles na III.
Manyan mutane daga faɗin duniya ne suka halarci bikin naɗin.
Sarki Charles III ya ce bai zama sarki domin mutane su riƙa yi masa bauta ba, ya zo ne domin ya yi wa al'umma bauta.
An saka wa Sarki Charles III kambi a matsayin sarkin Ingila wanda ya kai shekara 360 da ƙirƙira.
Kambin wanda ake yi wa laƙabi da Kambin Sarki Edward, an samar da shi a shekarar 1661 kuma Sarauniya Elizabeth II ce ta ƙarshe da ta saka shi shekara 70 da suka wuce.
Sarki Charles III ne basarake na bakwai da ya saka shi a tarihi kuma shi ma ba zai sake saka shi ba a rayuwarsa.
Mahaukaciyar guguwa da ta shafe fiye da wata ɗaya tana ɓarna
Haka ma, a wannan shekara da muke shirin bankwana da ita, wata mahaukaciyar guguwa ta afka wa ƙasashen Malawi da Madagascar da kuma Mozambique.
Guguwar tayi sanadiyyar mutuwar mutum sama da 400 da kuma ɗaiɗaita dubbai.
Guguwar ta kasance ɗaya daga cikin mafiya daɗewa da aka taɓa samu a yankin ko ma duniya baki ɗaya.
Kudancin Afirka ya sha faɗa wa cikin bala’o’in guguwa da ke zuwa daga tekun Indiya amma ita wannan ta sha bamban da irin waɗanda aka saba gani.
Ɓarkewar yaƙi a Sudan
A watan Afrilun wannan shekarar ta 2023, wani sabon rikici ya ɓarke a Sudan tsakanin sojojin ƙasar da kuma mayakan rundunar kai ɗaukin gaggawa ta RSF.
An kashe aƙalla mutum 7,000 a yaƙin.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce fiye da mutum miliyan biyar ne aka tilasta wa barin gidajensu, yayin da dama suka fice daga ƙasar.
MDD ta kuma ce kimanin rabin al'ummar ƙasar ne ke cikin yanayin buƙatar tallafi.
Sammacin kama Shugaba Putin na Rasha
Har ila yau, a wannan shekarar da muke bankwana, Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta aika takardar sammaci ga Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin, inda ake tuhumarsa da aikata laifukan yaƙi a Ukraine.
Ana kuma tuhumarsa da laifin tilasta wa ƙananan yara wajen tisa keyarsu daga Ukraine zuwa Rasha.
ICC tace akwai hujjoji da ta dogara da su da ke nuna cewa Mista Putin ya taka muhimmiyar rawa wajen tilasta wa yaran barin ƙasarsu tun bayan da Moscow ta fara ƙaddamar da hare-harenta kan Ukraine watanni 13 da suka gabata.
Fadar Kremlin ta bayyana sammacin da cewa abin takaici ne da kuma ba za a lamunta da shi ba.
Hamɓarar da shugaba Bazoum na Nijar daga kan mulki
A ranar 26 ga watan Yuli ne, sojoji suka sanar da karɓe iko a Jamhuriyar Nijar.
Wasu sojoji ƙalilan ne suka fito gidan talabijin na ƙasar suka tabbatar da juyin mulkin da suka yi.
Daga baya, sojojin sun sanar da naɗa Janar Abdourahmane Tchiani, a matsayin sabon shugaban ƙasar.
Ya kasance kwamandan rundunar tsaron fadar shugaban ƙasa tun daga shekarar 2011
Tun bayan yin juyin mulkin, suna ci gaba da tsare da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.
Duniya dai tayi Alla-wadai da juyin mulkin, musamman ma Majalisar Ɗinkin Duniya, da manyan shugabannin ƙasashen duniya, Bankin Duniya, Tarayyar Afrika da kuma Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afrika Ta Yamma (ECOWAS), inda suka kakaba wa Nijar ɗin takunkumai.
Indiya ta aika kumbonta na farko zuwa rana
Indiya ta samu nasarar harba kumbonta na farko zuwa rana, kwanaki kaɗan bayan da ƙasar ta kafa tarihin zama ta farko da kumbonta ya sauka a ɓaryar kudu na duniyar wata.
An harba mumbon mai suna Aditya-L1 daga tashar Sriharikota a ƙasar.
Kumbon zai yi tafiyar kilomita miliyan 1.5 daga doron duniya zuwa inda rana take.
Hukumar sararin samaniyar ƙasar ta ce kumbon zai yi tafiyar wata huɗu.
Shiga yajin aikin taurarin fina-finai a Amurka
Wani abu da ba za a manta da shi ba a shekarar 2023, shi ne tsunduma yajin aiki da Jaruman masana'antar fina-finan Hollywood ta Amurka da masu rubuta fina-finai suka yi a wani al'amari mafi girma cikin sama da shekara sittin.
Masu harkokin fim 160,000 ne suka dakatar da ayyuka a Los Angeles, abin da ya sa mafi yawan ayyukan fina-finai da shirye-shiryen talbijin suka tsaya cak.
Fasihan masu shirye-shiryen talbijin da rediyo na Amurka da ake kira Screen Actors Guild na neman manya-manyan kamfanoni masu dandalin kallon fina-finai ta intanet su amince da tsarin raba riba, sannan a kyautata yanayin aiki.
Ƙungiyar tana kuma son a kare jaruman fim daga yiwuwar maye gurbinsu da ƙirƙirarrun taurari na dijital.
Kaddamar da sabon dandalin sada zumunta na Threads
A watan Yuli ne, aka kaddamar da sabuwar manhajar sada zumunta ta Threads.
Shugabannin kamfanin Meta, Mark Zuckerberg ya bayyana dandalin da cewa kishiya ce "da za ta yi zaman mutunci" da Twitter, wadda hamshaƙin mai arziƙin nan Elon Musk ya saya.
Mutum miliyan goma ne suka yi rijista don amfani da sabuwar manhajar a sa'o'i kaɗan bayan kaddamar da shi a lokacin.
Ƙwararru sun ce dandalin Threads zai iya jan hankalin masu amfani da Twitter waɗanda ba sa farin ciki da sauye-sauyen da aka kawo wa manhajar a baya-bayan nan.
Trump ya zama shugaban Amurka na farko da aka ɗauki hotonsa a gidan yari
Donalad Trump ya zama shugaban Amurka na farko da aka ɗauki hotonsa a gidan yari bayan tsare shi na ɗan lokaci da aka yi a jihar Georgia inda ake yi masa shari'a bisa zargin yunƙurin sauya sakamakon zaɓen jihar a 2020.
An tilasta wa Mista Trump biyan dala 200,000 a matsayin kuɗin beli kafin sakin sa daga gidan kason na birnin Atlanta inda aka tsare shi na ɗan lokaci domin jiran yanke masa hukunci.
Daga baya dai Trump ya bayyana shari'ar da ake ma sa a matsayin "cin amana".
Girgizar ƙasa a Moroko
A watan Satumba ne girgizar ƙasa ta afka wa Moroko a wani yanki mai tsaunuka mai nisan kilomita 71 da garin Marakesh.
An kuma sake samun girgiza kasa mai karfin maki 4.9 bayan mintuna 19 a lokacin.
An samu asarar rayuka a Marrakesh da garuruwa da dama a kudancin ƙasar a cewar ma’aikatar cikin gida.
Girgizar ƙasar ta kashe mutum 600 a larduna da kananan hukumomi da ke al-Haouz, Marrakesh, Ouarzazate, Azilal, Chichaoua da kuma Taroudant.
Gine-gine da dama ne suka ruguje, yayin da tituna suka cika da ɓaraguzai.
Mutane sun yi ta guduwa da kuma shiga cikin firgici.
Ɓarkewar yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas
A ranar 7 ga watan Oktoba, mayakan Hamas suka kai wani hari mafi muni a shekarun baya-bayan nan kan Isra’ila.
Sun kai harin ne bayan kutsawa ta ɗaya daga cikin kan iyaka mafiya tsaro a doron kasa.
A lokacin, an ruwaito cewa mutum 250 ne suka mutu, yayin da wasu 1,100 suka samu raunuka bayan harin da ƙungiyar Hamas ɗin ta kai.
Nan da nan, Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar kai harin ramuwar gayya zuwa cikin Zirin Gaza.
Hukumar lafiya ta Hamas a Gaza, ta ce an kashe kusan Falasɗinawa 18,000 a yanzu.
Ɓacewar sunduƙin yawon shaƙatawa na ƙarƙashin teku
A cikin wannan shekarar da ke shirin karewa ne dai, wani sunduki mai tafiya a ƙarƙashin teku don ganin tarkacen jirgin Titanic ya ɓace a can ƙarƙashin tekun Arewacin Atalantika.
Mutum biyar ne ke cikin jirgin lokacin da ya ɓace.
Masu bincike a cikin jirgin ruwan Polar Prince - babban jirgin da ke ɗauke da sunduƙin zuwa ƙarƙashin teku daga saman ruwa - ya rasa sadarwa da ma'aikatan jirgin jim kaɗan bayan ya fara nutso a cikin teku.
Iskar numfashi ta oksijin da ke cikin jirgin taƙaitacciya ce.
A lokacin, jami'an tsaron gaɓar tekun Amurka sun aika wasu jiragen ƙarƙashin teku da ake sarrafa su daga nesa, don gudanar da bincike a farfajiyar wurin.