Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Matsalar rashin zaman mabiyiya yadda ya dace a mahaifa
Wurin da mabiyiya ta zaɓa don ta zauna a jikin mahaifa don ta girma kan janyo rasa ran jariri da mai juna biyu.
Mabiyiya na da matuƙar muhimmanci a goyon ciki, domin ita ce ke samar da jini da sinadaren da ɗantayi ke buƙata a tsawon lokacin da yake cikin mahaifiyarsa.
Sai dai idan ta zauna a kan bakin mahaifa ta kan hana jariri fita a lokacin naƙuda.
Yayin da kuma ta kan janyo zubar jini matuƙa ga mai juna biyu.
Waɗannan matsaloli biyu na daga cikin manyan dalilan da ke janyo mutuwar uwa da kuma jariri.
Hanzarta yi wa mai wannan matsalar da jini ya tsinkewa tiyatar haihuwa na daga cikin manyan hanyoyin da ake bi don ceton rayukan masu ciki da na jarirai a asibiti.
To waɗanne abubuwa ne ke ƙara haɗarin mabiyiya ta zauna a kan bakin mahaifa?
latsa makunnin da ke sama domin jin cikakken bayani daga baki wata ƙwararriyar likitar mata a Najeriya, Dr. Rabi'a Mahmud.