Lafiya Zinariya: Yadda za ki tsaftace ƙunzugun da ake ɗinkawa 01/02/2025

Lafiya Zinariya: Yadda za ki tsaftace ƙunzugun da ake ɗinkawa 01/02/2025
An wallafa

Masana a fannin kiwon lafiya sun yi ƙarin haske kan yadda ya kamata mace mai jinin al'ada ta tsaftace ƙunzugun da take amfani da shi.

Hanyoyin sun ƙunshi waɗannan matakai na ƙasa:

  • Wanke jinin a zubar da ruwan a magudanan ruwa , ko salga ko masai na gargajiya.
  • A sake wanke shi ta hanyar amfani da sabulu ko garin sabulu da ruwa.
  • A ɗauraye shi da ruwa a shanya a rana domin ya bushe.
  • Ana kuma iya amfani da dutsen guga wajen goge shi, domin kashe kwayoyin cuta.
  • Aƙalla ya kamata mace ta tanadi ƙunzugun guda huɗu ta yadda za ta iya cirewa ta sanya wani.
  • Ana kuma iya cire shi ne bayan sa'oi uku zuwa 12, amma ya danganta da yawan jinin da ke zuba.

Haka kuma ba a so ƙunzugu ya wuce sa'oi 12 ba tare da an sauya shi ba, ko da kuwa bai jiƙe ba.

Idan mace ba ta tsaftace ƙunzugun yadda ya kamata ba, ko kuma ta bar shi ya daɗe sosai a jikinta ba tare da ta sauya shi ba, hakan zai iya haifar mata da wasu matsaloli ta ɓangaren kiwon lafiya.

Kuma idan lamarin ya tsananta, yakan iya janyo wa mace samun ciki a bayan mahaifa, ko rashin ɗaukar ciki ko matsanancin ciwon mara ko na baya a tsawon rayuwarta.