Kafar Real Madrid ɗaya ta kai wasan karshe a Copa del Rey

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid ta je ta ci Real Sociedad 1-0 a wasan farko na daf da karshe a Copa del Rey ranar Laraba.

Minti na 19 da fara wasan ne, Real ta ci ƙwallon ta hannun Endrik ɗan kasar Brazil.

Karo na biyu da suka fuskanci juna a bana, bayan da Real ta je ta yi nasara 2-0 a La Liga cikin Satumbar bara.

Wannan shi ne karo na biyu da suka kara a Copa del Rey a tsakaninsu, bayan da Sociedad ta je ta yi nasara a kan Real da cin 4-3 ranar Alhamis 6 ga watan Fabrairun 2020.

Real ta kawo wannan matakin, sakamakon da ta doke Leaganes 3-2 cikin watan nan, ita kuwa Sociedad 2-0 ta yi nasara a kan Osasuna.

Real Madrid ta buga wasan na ranar Laraba ba tare da Kylian Mbappe da Federico Valverde da kuma Thibaut Courtois ba.

Real mai rike da kofin La Liga da Champions League na fatan lashe Copa del Rey na 21 jimilla, wadda za ta karɓi bakuncin wasa na biyu ranar 1 ga watan Afirilu.

Ƴan wasan da suka buga wa Real karawa da Sociedad:

Masu tsare raga: Lunin, Fran González da kuma Mestre.

Masu tsare baya: Alaba, Lucas V., Fran García, Rüdiger, Mendy da kuma Asencio.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Modrić, Tchouameni, Arda Güler, Ceballos da Chema.

Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Rodrygo, Endrick, Brahim da kuma Gonzalo.