Super Eagles ta gayyaci ƴan Kano Pillars uku har da Rabi'u Ali

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kociyan Super Eagles, Austin Eguavon ya gayyaci ƴan Kano Pillars uku ciki har da Rabi'u Ali, domin karawa da Ghana a neman shiga gasar CHAN 2025.

Sauran da aka kira daga Pillars sun haɗa da Abiam Nelson da kuma Adams Aminu Sani a tawagar ta Super Eagles masu taka leda a gida.

Rabi'u Ali yana kan ganiya a wasannin Premier ta Najeriya ta bana, wanda ya zura ƙwallo takwas a raga, bayan kammala wasannin mako na 15.

Ana sa ran ƴan wasan da aka gayyata za su je katafaren filin wasa na Remo Stars a Ikenne da ke jihar Ogun daga ranar 4 ga watan Disamba, domin karbar horo.

Super Eagles za ta fara zuwa Ghana a wasan farko ranar 22 ga watan Disamba, sannan a buga fafatawa ta biyu ranar 28 ga watan Disamba a Godswill Akpabio Stadium a Uyo jihar Akwa Ibom.

Za a buga gasar CHAN 2025 ta ƴan wasan da ke taka leda a gida a cikin watan Fabrairun 2025 a Kenya da Uganda da kuma Tanzania.

Ghana ta yi wa Super Eagles kancal a zuwa gasar CHAN a 2009 da kuma 2023, inda Najeriya ta zama ƴar kallo.

Ƴan wasan da aka gayyata domin neman shiga gasar CHAN:

Masu tsare raga: Henry Ozoemena (Enyimba FC), Kayode Bankole (Remo Stars), Nurudeen Badmus (Kwara United)

Masu tsare baya: Ismail Sadiq (Remo Stars), Waliu Ojewole (Ikorodu City), Imo Obot (Enyimba FC), Taiwo Abdulrafiu (Rivers United), Junior Nduka (Remo Stars), Victor Collins (Nasarawa United), Ifeanyi Onyebuchi (Rangers International), Steven Mayo (Rivers United)

Masu wasa daga tsakiya: Jide Fatokun (Remo Stars), Rabiu Ali (Kano Pillars), Saviour Isaac (Rangers International), Musa Zayyad (El-Kanemi Warriors), Emmanuel Ogbole (Kwara United), Papa Daniel Mustapha (Niger Tornadoes), Kazeem Ogunleye (Rangers International)

Masu cin ƙwallaye: Anas Yusuf (Nasarawa United), Adamu Abubakar (Plateau United), Osy Martins (Lobi Stars), Sikiru Alimi (Remo Stars), Temitope Vincent (Plateau United), Samuel Ogunleye (3SC), Abiam Nelson (Kano Pillars), Meyiwa Oritseweyimi (Bendel Insurance), Ngbemena Ikechukwu (Heartland FC), Sunday Megwo (Abia Warriors), Umar Al-Amin Ibrahim (El-Kanemi Warriors), Adams Aminu Sani (Kano Pillars).