Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hikayata: Labarin Biyu Babu
A ci gaba da kawo muku labarai 12 da alƙalan gasar Hikayata suka ce sun cancanci yabo, a yau za mu kawo muku labarin Biyu Babu na Zainab Abdurrahman Aminu daga jihar Katsina wanda Aisha Sharif Baffa ta karanta.
Marubuciyar labarin ta gina shi a kan wata yarinya mai suna Sadiya, da ta yi biyu babu a lokacin da ta biye wa sharrin zuciya, ta ƙi ɗan'uwanta - wanda aka yi musu alƙawarin aure, ta biye wa saurayi ɗan ƙarya.
Bayan sun yi aure da ɗan'uwan nata ta ƙi yin biyayyar aure, ta shiga saɓa wa Allah da mijinta ta hanyar cin amanar aure ita da saurayin da take so.
A ƙarshe dai ta tashi a tutar babu ta hanyar yin biyu babu, a dalilin mijin da saurayin duk sun guje ta.