Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Copa del Rey: Sociedad da Real Madrid da na Barcelona da Atletico
Real Madrid za ta fuskanci Real Sociedad a zagayen daf da karshe a Copa del Rey karawar daf da karshe a jadawalin da aka fitar ranar Laraba.
Ƙungiyar Santiago Bernabeu ta kawo wannan matakin, bayan da ta je ta doke Leganes 3-2 ranar Laraba 2 ga watan Fabrairu.
Ita kuwa Sociedad kuwa nasara t yi a kan Osasuna da cin 2-0 ranar Alhamis 6 ga watan Fabrairu a zagayen kwata fainal.
A gasar La Liga ta bana, Real ta je ta ci Sociedad 2-0 ranar Asabar 14 ga watan Satumbar 2024, Vinicius Junior da Kylian Mbappe ne suka ci ƙwallyen a bugun fenariti.
Za su kara a wasa na biyu a La Liga ranar wasan karshe da za a rufe labulen gasar, inda Real za ta karɓi bakuncin Sociedad ranar Lahadi 25 ga watan Mayun 2025.
Ɗaya wasan daf da karshe a Copa del Rey da za a yi gida da waje shi ne wanda za a kece raini tsakanin Barcelona da Atletico Madrid.
A gasar La Liga a bana, Barcelona ta yi rashin nasara a gida da ci 2-1 a hannun Atletico Madrid ranar Asabar 21 ga watan Disambar 2024.
Sai a ranar Lahadi 16 ga watan Maris Atletico Madrid za ta karɓi bakuncin Barcelona a babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta kakar nan.
Real Madrid ce ta ɗaya a kan teburin La Liga da maki 50 da Atletico ta biyu mai maki 49 da Barcelona ta uku mai maki 48 da kuma Sociedad mai maki 31 ta bakwan teburi.
Za a fara wasannin farko a daf da karshe a Copa del Rey ranar 25 ko 26 ko kuma 27 ga watan Fabrairu, za a buga karawa ta biyu tsakanin 1 ko 2 ko kuma 3 ga watan Afirilu.
Jadawalin daf da karshe a Copa del Rey:
- Barcelona da Atletico Madrid
- Real Sociedad da Real Madrid