Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ra'ayi Riga: Kan kashe-kashen gaban kai 04/04/2025
A shirinmu na Ra'ayi Riga wannan makon, mun nazari ne kan kashe-kashen gaban kai wanda ake kira 'jungle justice' da Ingilishi.
A kwanakin baya ne dai aka kashe wasu mtafiya kusan 16 mafarauta ƴan arewa a jihar Edo da ke kudancin ƙasar, lamarin da ya jawo maganganu da muhawara a ƙasar.
Sai dai ba shi ba ne karo na farko da ake samun irin wannan yanayi, inda mutane suke ɗaukar doka a hannunsu.
Shin me yake irin wannan matsala?
Me yake sa mutane suka ɗaukar doka a hannunsu?
Shin akwai gazawar jami'an tsaro?
Me ya kamata gwamnati ta yi?
Waɗannan na daga cikin batutuwan da muka tattauna a cikin shirin namu na Ra'ayi Riga na wannan makon.