Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An amince gola ya riƙe ƙwallo daƙika takwas daga baɗi
An amince mai tsaron raga ya riƙe ƙwallo daƙika takwas, maimakon shida daga kakar baɗi.
Ana hukunta duk golan da ya riƙe tamaula fiye da minti shida da bugun tazara, amma ba kasafai ake hukunci kan laifin ba.
Tun a wannan kakar ana barin masu tsare ragar su riƙe ƙwallon minti takwas har da a gasar Championship, domin gwaji kafin kaka mai zuwa.
Rafli kan ƙidaya sauran daƙika biyar da yatsunsa, an kuma samu sauyi da bayar da bugun kwana, maimakon bugun tazara.
Tuni dai mahukuntan tamaual suka amince da gwajin da ake yi, sun kuma yadda dokar ta fara aiki a 2025-26.
Haka kuma an amince da sabuwar dokar satar fage, wadda ta ce rafli ba zai hura ba da zarar kafaɗar ɗan wasa ta yi daidai da mai tsaron baya daga shi ba kowa.