Yadda za ku kare kanku daga cutar shawara

Yadda za ku kare kanku daga cutar shawara
An wallafa

Miliyoyin mutane a nahiyar Afrika na fuskantar barazanar kamuwa da cutar shawara, wanda sauro ke janyowa.

Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce nau’in sauron da ke janyo cutar shawara da rana yake cizo, kuma yana yaduwa ne a gidaje da kuma cikin dazuka.

Inda hukumar ta bayyana cewa allurar rigakafi, ita ce babbar hanyar kare kai daga cutar.

Haka kuma likitoci sun jaddada muhimmancin tsaftace muhalli don ka da a bai wa sauro damar yaduwa.

Sannan kwanciya a gidan sauro mai feshin magani da sanya maganin kashe sauro a wurin kwana, suna daga cikin hanyoyin kare kai daga cutar shawarar.

Ko da yake mutane da yawa masu dauke da cutar ba sa nuna alamominta, amma ga wadanda alamomin ke bayyana, sun hada da zazzabi da ciwon jiki da ciwon kai da ciwon baya da rashin son cin abinci da tashin zuciya da amai.

Idan cutar ta yi kamari ta kan shafi hanta da koda, kuma ta kan sauya launin jiki zuwa kore, sannan ta kan kai ga zuban jini har da asarar rayuka.

Alkaluman WHO, sun nuna cewa kimanin ‘yan Najeriya miliyan 160 ne ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar, adadin da ya kai kashi 25 cikin dari na mazauna nahiyar Afrika.

Cutar shawara ta yellow fever ta fi kamari a Afrika da kuma tsakiya da kudancin Amurka.