Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Illolin rashin isasshen bacci ga yara 27/07/2024
Isasshen bacci mai kyau na taimakawa wajen tsaftace ƙwaƙwalwa da tattara abubuwan da suka faru domin adana su na dogon lokaci, sannan yana kuma bunƙasa basira.
Sai dai rashin isasshen baccin ko kuma bacci mara inganci kan shafi lafiyar jiki da ta ƙwaƙwalwa da kuma walwala.
Gidauniyar da ke bincike tare da samar da bayanai kan bacci ta Amurka, ta bayyana yawan baccin dare da ya kamata rukunin mutane su samu.
A cewarta, yaran da ba su fara zuwa makaranta ba zuwa masu shekara 12 a duniya, suna buƙatar samun bacci na tsawon sa’oi 10 zuwa 11 a duk dare.
Yayin da ƙwararrun likitocin yara suka jaddada muhimmancin sanya lokacin bacci ga yara don tabbatar da sun samu ƙoshin lafiya.
Sun kuma yi nuni da samun baccin mai inganci don zai taimaka wajen kare yara daga saurin kamuwa daga cututtuka kana ya kare su daga illolin da rashin samun bacci mai kyau ke haifarwa.
A cikin shirin Lafiya Zinariya na wannan makon mun tattauna da wata likitar yara da ke aiki a Ingila, Dr. Sadiya Gumi kan wannan batu.
Sai a saurari shirin domin samun cikakken bayani.