Gane Mini Hanya: Hira da Kwankwaso

Gane Mini Hanya: Hira da Kwankwaso
An wallafa

Ɗaya daga 'yan takarar shugabancin Najeriya a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun bana, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya ce jam'iyyarsa ta NNPP ta yi rawar gani a zaɓen duk da cewa shi ne ya zo na huɗu a jerin waɗanda suka samu ƙuri'u mafiya yawa.

Kwankwaso ya ce sakamakon zaɓen zai bai wa jam'iyyarsa damar amfani da darussan da ta ɗauka a yayin zaɓen da kuma gyara kura-kuren da ta yi.

Kuma kamar yadda za ku ji a cikin wannan hira da musamman da Yusuf Ibrahim Yakasai, Rabiu Kwankwaso ya ce da jam'iyyar ta samu jajirtattun shugabanni a jihohin ƙasar, da ta samu nasara irin wacce ta samu a jihar Kano.

Sai dai Yusuf Yakasai ɗin ya fara da tambayar Kwankwason kan yadda ya kalli yadda zaɓen ya gudana.