Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya:Yadda ƙunzugun da ake ɗinkawa ke samun karɓuwa 11/01/25
Kimanin mata fiye da biliyan biyu ne ke jinin haila duk wata a faɗin duniya, a cewar hukumar da ke kula da harkar mata ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
Sai dai kimanin biliyan ɗaya da rabi basu da ƙunzugun da za su yi amfani da shi da sauran abubuwan da suke buƙata don kasancewa cikin tsafta a yayin da suke al'ada.
Amma wasu manyan hukumomi na duniya ciki har da Asusun tallafawa ƙananan yara na majalisar da ƙungiyoyin fareren hula sun duƙufa wajen koyar da ƙunzugun da ake ɗinkawa tare da raba shi a tsakanin mata.
Duk da cewa wasu al'umomi sun rungumi amfani da wannan ƙunzugu, a cewar ƙungiyoyin har yanzu akwai ɓukatar wadata mata masu shekarun al'ada da ƙunzugun da ruwa da kuma makewayi don tsaftace kansu.