Cututtukan da suka fi addabar yara a lokacin damuna

Cututtukan da suka fi addabar yara a lokacin damuna
An wallafa

Danna hoton da ke sama don sauraron shirin:

A lokacin damuna, yara da dama na jin dadin saukar ruwan sama, domin su kan shiga su yi wasa idan yana sauka ko kuma a cikin wanda ke kwance, sai dai hakan na da hatsari ga lafiyarsu.

Sannan a wannan lokaci ne yara kan kamu da wasu cututtuka kamar zazzabin cizon sauro, zazzabin typhoid, kwalara, mura da zazzabi, nimoniya da dai sauransu.

Masana a fannin kiwon lafiya sun ce yara na saurin kamuwa da kwayoyin cuta ne, saboda kankantarsu da kuma rashin garkuwar jiki mai karfi.

Wasu yankunan Afrika na daga cikin wurare a duniya da ke fuskantar mamakon ruwan sama da ke kai wa ga ambaliyar ruwa duk shekara.

Hukumar lafiya ta duniya reshen Afrika ta ce, a shekarar 2020 yara ‘yan kasa da shekara biyar su ne kashi 80 cikin dari na mutuwar da aka samu a nahiyar, a sanadiyyar cutar zazzabin cizon sauro.