Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fulham ta taka wa Liverpool burki bayan wasa 26 a jere ba a doke ta ba
Fulham ta kawo kashen Liverpool, wadda ta yi wasa 26 a jere ba tare da rashin nasara ba a Premier League a kakar nan.
Fulham ta yi nasarar cin Liverpool 3-2 a Craven Cottage ranar Lahadi a wasan mako na 31 a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Lahadi.
Ƙungiyar da Arne Slot ke jan ragama ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Alexis Mac Allister daga baya Fulham ta ci uku a minti 13 tun kan hutu.
Ryan Sessegnon ne ya farkewa daga baya Fulham ta kara na biyu ta hannun Alex Iwobi, sannan Rodrigo Muniz ya kara na uku.
A zagaye na biyu ne Liverpool ta zare ɗaya ta hannun Luis Diaz a minti na 72, haka Liverpool ta yi ta kokarin kara na uku amma hakan bai samu ba.
Rabon da Liverpool ta yi rashin nasara a Premier League a kakar nan tun bayan doke ta 1-0 da Nottingham Forest ta yi a Anfield ranar 14 ga watan Satumbar 2024.
Liverpool ta ci gaba da zama ta ɗaya a teburin Premier League da tazarar maki 11 tsakani da Arsenal ta biyu.
Ita kuwa Fulham ta samar da damar shiga cikin masu wakiltar Ingila a gasar zakarun Turai, bayan da take mataki na takwas da tazarar maki biyar tsakani da Chelsea ta huɗu.