Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Darussa biyar da Najeriya za ta koya daga zaɓen shugaban ƙasar Ghana
- Marubuci, Daga Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Duk lokacin da aka gudanar da zaɓe mai inganci a wata ƙasa musamman mai maƙwabtaka da Najeriya, sai ka ji masana na cewa ya kamata ƙasar mafi yawan al'umma a nahiyar ta yi koyi.
Wannan ba abin mamaki ba ne ganin yadda har yanzu ake shakku game da sahihancin zaɓuka a Najeriya bayan shekara 23 a jere kan turbar dimokuraɗiyya.
Ƙasar Ghana ce ta baya-bayan nan - wadda ƙawar Najeriyar ce ta kusa kuma 'yar'uwa mamba a ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma wato Ecowas - da ta abar misali.
A ranar Litinin hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da ɗantakarar adawa na jam'iyyar NDC, tsohon Shugaban Ƙasa John Mahama, a matsayin wanda ya kayar da na jam'iyyar NPP mai mulki, Mataimakin Shugaban Ƙasa Mahamudu Bawumia.
'Yantakara 12 ne suka fafata a zaɓen, sai dai takarar ta fi zafi tsakanin tsohon shugaban ƙasar, da kuma mataimakin shugaban ƙasar mai-ci - kusan dai kamar yadda aka yi a zaɓen Amurka na 2024.
Shugaban Ƙasa Nana Akufo-Addo zai sauka daga mulki ne bayan ya yi wa'adin shekara huɗu sau biyu.
Mun tuntuɓi Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin kimiyyar siyasa na Jami'ar Bayero ta Kano, domin jin darussan da masana ke ganin Najeriya za ta koya daga zaɓen na Ghana.
Sharhi daga Farfesa Kamilu Sani Fagge
Liƙa fasta ko'ina
Najeriya da ma ƙasashen Afirka na da abubuwa da yawa da za su koya daga wannan zaɓe.
Lokacin da ake yin zaɓen, idan ka je ba za ka ga an lilliƙe ko'ina da hotunan 'yantakara ba kamar hauka - irin yadda muke yi a Najeriya.
Allunan ɗantakara na kowace jam'iyya kawai za ka gani. Idan aka saka ɗaya sai an yi tafiya kamar kilomita ɗaya, ko rabin kilomita kafin ka sake ganin wani.
Kuma haka ake yi tun daga yaƙin neman zaɓe har zuwa bayan zaɓen.
Kishin ƙasa da mutunta juna
Darasi na biyu shi ne yadda 'yantakara su kansu suka girmama juna.
Tun kafin a kammala ƙirga ƙuri'u Mataimakin Shugaban Ƙasa Bawumia ya kira Mahama don ya taya shi murna sabda sun fahimci cewa ba za su yi nasara ba a zaɓen.
Hakan ya nuna cewa ƙasarsa ta Ghana ce a gabansa ba buƙatarsa ba. Da mu ne a nan, da tuni an fara zargin maguɗi kuma da ƙarshe a je kotu a yi ta jan maganar.
Dalilin da ya sa ba a fiya samun haka ba a Najeriya shi ne yadda muka mayar da siyasa batun ko a mutu ko a yi rai.
Magana ce ta kishin ƙasa saboda Ghana ta daɗe tana samun irin waɗannan shugabanni.
Doka da oda
Duk inda dimokuraɗiyya ta yi nasara to akwai maganar doka da oda.
Gaskiya hukumar zaɓensu ta yi aikinta a matsayin kamar lafari - kamar yadda ake faɗa a harkar ƙwallon ƙafa - wato alƙali a wurin gudanar da zaɓen.
Wannan darasi ne babba da za mu koya wajen gudanar da abubuwa a tsare kuma cikin adalci.
Sharhi daga Umar Mikail
Yawan masu kaɗa ƙuri'a
Shugabar hukumar zaɓe ta Ghana, Jean Mensa, ta ce kashi 60.9 cikin 100 na mutum fiye da miliyan 18 ne da ke da rajista suka fita kaɗa ƙuri'ar.
Wannan adadi ya ninka na 'yan Najeriya sau biyu da ɗoriya (29 cikin 100) na waɗanda suka fita kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa na Fabrairun 2023.
Shi kansa kashi 60.9 da Ghana ta samu a zaɓen na bana ragi aka samu a kan na zaɓen 2020, inda kashi 79 suka fita kaɗa ƙuri'ar.
A Najeriya kuwa, lamarin ya fi lalacewa saboda yadda adadin yake ta raguwa tun daga 2011, inda aka samu kashi 53.68%, da 2015 (47.09%), da 2019 (35.66%).
Sayen ƙuri'a
Ɗaya daga cikin matsalolin da ke mamaye zaɓe a kowane mataki a Najeriya shi ne sayen ƙuri'a.
Sai dai a wannan zaɓen na Ghana ba mu samu wasu rahotonnin da ke nuna sayen ƙuri'un ba.
Baya ga wakilan BBC Hausa biyu - Haruna Tangaza da Usman Minjibir - da suka je ɗauko rahoto kan zaɓen, akwai sauran wakilan BBC da suka karaɗe sassan ƙasar da dama, kuma babu wanda ya bayar da rahoton cinikin ƙuri'u a filin Allah.
Duk da cewa ba mu da tabbas game da ko an sayi ƙuri'ar ko ba a saya ba, ba a ji rahotonnin hakan ba a kafofin yaɗa labarai kamar yadda aka saba a Najeriya.