Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda za a kauce wa kamuwa da cutukan al'aurar yara mata 28/12/2024
Yin tsarki bayan an yi fitsari da bayan gari yadda ya kamata na daga cikin hanyoyin da ke kare yara mata daga kamuwa da wasu cututtukan al'aura, in ji likitoci.
Yara mata waɗanda basu kai shekarun balaga ba, kan samu irin waɗannan cututtuka, lamarin da ke haifar da damuwa ga iyaye.
Masana a fannin kiwon lafiya sun ce cututtukan al'aura akwai waɗanda ake samunsu ta hanyar jima'i, sannan akwai waɗanda ake ɗauka kai tsaye ta hanyar ƙwayoyin cuta.
Likitoci sun bayyana cewa yadda ya kamata a yi tsarki ga mace ko namiji shi ne, a fara da yin tsarkin fitsari sannan a yi na bayan gari, sai a wanke hannu ba tare da an sake taɓa wajen fitsarin ba.
Sannan sun jaddada muhimmancin wanke hannu kafin a yi tsarki da kuma bayan an gama don kaucewa ɗaukar ƙwayoyin cuta.
Dr. Hadiza Ashiru wata likitar yara a Najeriya ta yi cikakken bayani kan tsarki da yadda rashin yinsa da kyau kan kai ga ciwon ƙoda.