Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gagarumin aikin da ke gaban masu sake gina Zirin Gaza
- Marubuci, Paul Brown
- Marubuci, Kayleen Devlin
- Marubuci, Erwan Rivault
- Marubuci, Barbara Metzler
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Yayin da dubun dubatar mazauna Zirin Gaza ke komawa gidajensu bayan yarjejeniyar tsagaita wuta, akasarinsu na sane da cewa gidajen nasu sun zama ɓaraguzai.
Aikin sake gina gidaje, da wuraren harkoki ba ƙaramin abu ba ne. Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta yi ƙiyasin ɓarnar ta kai ta dala biliyan 70.
Kamar yadda Farfesa Andreas Krieg, wani ƙwararre kan harkokin Gabas ta Tsakiya a jami'ar King's College London, ya bayyana: "Lamarin ya fi muni fiye da a ce za a fara aikin daga farko - a yanzu za a fara aikin ne da ɓaraguzai maimakon dandariyar ƙasa."
Yawan ɓarnar da aka yi a zirin yanzu ta kai "kashi 84 cikin 100. A wasu yankunan ma kamar Birnin Gaza, ta kai kashi 92", a cewar Jaco Cilliers, ƙwararre kan ayyukan cigaba na MDD a Falasɗinu.
Nazarin da sashen BBC Verify ya yi bayan duba bayanai daga tauraron ɗan'adam ya nuna cewa yawan ɓaraguzan zai kai kusan tan miliyan 60 da za a share daga zirin.
Ba za a iya fara komai ba ba tare da an share ɓaraguzan ba.
Share ɓaraguzai
Miliyoyin tan na ɓaraguzai da ke Gaza ba wai kankare ba ne kawai da rodina. Akwai gawawwakin mutane da kuma bamabaman da ba su fashe ba.
"Idan ana maganar zaman lafiya, abin da za a fara yi shi ne tabbatar da kwashe ababen fashewar da ke wuraren da aka kai wa hare-hare," in ji Philip Bouverat, tsohon shugaban cibiyar JCB.
Sai kuma a shiga tantancewa, da warewa, da kuma kwashe ɓaraguzan. Bayan an ware abubuwa kamar robobi da ƙarafuna, za a iya amfani da kankaren a matsayin mafarin gini.
"Ba za a iya yin wannan da motoci ba. Abu na farko shi ne gina tashar gaɓar ruwa, ta haka ne za a iya shigo da dubban kwantenoni ɗauke da kayayyaki," kamar yadda Mista Bouverat ya ƙara da cewa.
Ruwa da hanyoyin bahaya
Ruwna sha na ɗaya daga cikin manyan buƙatun mazauna Gaza. A cewar hasashen Unicef, sama da kashi 70 cikin 100 na cibiyoyin samar da ruwan sha sun lalace ko kuma an tarwatsa su tun daga 7 ga watan Oktoban 2023.
Bayan sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta, sojojin Isra'ila sun ɗauki hotuna a kusa da wata cibiyar tace ruwa, wadda aka lalata jim kaɗan kafin su fice daga zirin.
Likitoci sun ce ana yawan kamuwa da amai da gudawa a Gaza, wadda ke yawan kashe yara, saboda lalacewar hanyoyin fitar bahaya da suka fantsama cikin gari.
Akwai cibiyoyin tace ruwa shida a Gaza. "An lalata dukkansu," kamar yadda Maher Najjar, mataimakin shugaban cibiyar Coastal Municipalities Water Utility (CMWU), ya bayyana.
Tun bayan fara yaƙin, yawan kai hare-hare sun sa an kasa gyara cibiyoyin da aka lalata, da kuma ƙarancin kaya aikin yin hakan. Wasu kuma an sake lalata su bayan gyarawa.
Rundunar sojin Isra'ila na cewa tana yin hakan ne bisa dokar ƙasashen duniya" saboda ta daƙile shirin Hamas "na cutar da Isra'ilawa.
Akwia kuma cibiyoyin da ke samar da ruwan shan a Gaza, waɗanda su ma suka fuskanci babbar matsala.
"Jimillar asarar da aka yi ta kai dala biliyan ɗaya, ko fiye da haka," in ji Mista Najjar.
Gidaje
Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna ɓarnar da aka yi a unguwar Sheikh Radwan da ke arewacin Birnin Gaza.
A watan Agusta kafin Isra'ila ta mamaye birnin, da yawan titunan wurin lafiya ƙalau suke. Zuwa makon da ya wuce, an ɗaiɗaita unguwannin da ke kusa kafin daga baya rundunar sojin Isra'ila IDF ta kafa sansani.
Cibiyar tauraron ɗan'adam ta MDD mai suna Unosat ta yi ƙiyasin cewa an rushe ko lalata gidaje a Gaza da suka kai 282,904.
Amma akwia yiwuwar wannan adadi ya yi ƙasa sosai, domin ba a haɗa da ɓarnar da aka yi ta baya-bayan nan ba a Birnin Gaza kamar irin ta unguwar Sheikh Radwan.
Hukumar Birnin Gaza ta ce an lalata kashi 90 na titunan yankin.
Shelly Culbertson ta cibiyar RAND Corporation da ke birnin Washington na ganin sake gina Gaza zai ɗauki tsawon shekaru.
"Bayan hare-haren Isra'ila a 2014 da 2021, aikin sake gina yankin bai yi sauri ba saboda Isra'ila ta ƙi bari a shigar da kayayyaki da yawa bisa fargabar ana iya yin amfani da su a wata hanyar daban," a cewarta.
"Idan za a bi irin hanyar da aka bi a 2014 da 2021, zai ɗauki shekara 80. Idan an yi shiri mai kyawu ba zai ɗauki lokaci mai yawa ba," kamar yadda ta bayyana.
Lantarki
Tun kafin yaƙin nan da ma Gaza ke fuskantar matsalar lantarki. Ana yawan ɗauke wuta kuma mazauna Gaza da yawa na zaune cikin duhu a wasu awanni na kowace rana.
Akasarin lantarkin zirin na zuwa ne daga Isra'ila, da tashoshin da ke amfani da man dizel, da kuma allunan lantarki daga hasken rana a wasu ma'aikatun gwamnati da aka samu a kwanan nan.
Kusan baki ɗayan Gaza ya auka cikin duhu bayan Isra'ila ta katse lantarki tun daga 11 ga watan Oktoba, in ban da wata cibiyar samar da ruwan sha a Birnin Gaza. Isra'ila ta kunna wutarta ranar 14 ga watan Nuwamban 2024, sannan ta sake kashewa ranar 9 ga watan Maris 2025, kafin ta sake kunnawa.
Saboda kashe wutar, yanzu ayyuka masu muhimmanci sun dogara ne kan injinan lantarki masu amfani da dizel da kuma 'yan allunan solar da suka rage.
Noma
Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna yadda aka lalata gonar inibi ko lemon tsami mai girman murabba'in kilomita 4 a unguwar Jabalia.
Sojojin Isra'ila sun samar da hanyoyi daban-daban ta cikin gonaki domin shiga unguwannin da ke kusa da Birnin Gaza.
Nazarin da Farfesa He Yin na Jami'ar Kent ya yi ya bayyana cewa an lalata kashi 82.4 cikin 100 na amfanin shekara-shekara a Gaza da kuma kashi 97 na bishiyoyi zuwa ranar 10 ga watan Agusta na shekarar nan.
Mista Bouverat ya ce idan ana so a gyara al'amura sai an kwashe bamabaman da ba su fashe ba tukunna cikin gaggawa. "Idan za su iya cigaba da noma za su iya ciyar da kan su, kuma zai fi kyau idan aka yi hakan cikin hanzari."
Ilimi
Kusan rabin al'ummar Gaza kafin yaƙin 'yan ƙasa da shekara 18 ne, saboda haka gyara makarantu na da muhimmanci sosai.
Makarantu ne suka zamar wa mutane mafaka kuma duk da haka Isra'ila ta yi ta kai musu hari tana iƙirarin cewa "cibiyar soja ce ta Hamas".
Hukumar bayar da agaji ta MDD a Falasɗinu Unrwa ta ce kashi 91.8 cikin 100 na gine-ginen makarantu a Gaza za su buƙaci sake gina su ko kuma gagarumin gyara.
A watan Disamban 2023 dakarun Isra'ila suka tarwatsa ginin Jami'ar Al-Azhar da ke kudancin Birnin Gaza.
Haka lamarin yake a Jami'ar Israa mia nisan kilomita biyu kacal daga Azhar bayan sun yi amfani da ginin a matsayin sansani na 'yan makonni.