Al'ummar da ke da harshen mata daban da na maza a Najeriya

Al'ummar da ke da harshen mata daban da na maza a Najeriya
An wallafa

Yayin da sauran al'ummomi daban-daban na duniya ke amfani da harshe daya tsakanin mata da maza wajen zantuka da mu'amalar yau da kullum, abin ba haka yake ba a garin Ubang na yankin Ƙaramar Hukumar Obudu ta jihar Kuros Riba da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Mutanen garin na Ubang na amfani ne da harsuna biyu, wato harshen maza daban na mata kuma daban.

Da haka suke zantawa da juna yau da kullum kuma suke fahimtar juna.

Abdussalam Ibrahim Ahmed ya ziyarci garin kuma ya aiko rahoto na musamman.