Kotu ta haramta wa Trump tsayawa takara

An wallafa

Kotun kolin Colorado ta yanke hukuncin cewa Donald Trump ba zai yi takarar shugabancin Amurka ba a jihar, a shekara mai zuwa, tana mai dogaro da wani sashe na kundin tsarin mulkin kasar kan yin bore ga hukumomi.

Kotun wadda alkalanta hudu bisa uku suka amince da hukuncin cewa Mr. Trump bai cancanta tsayawa a matsayin dan takara ba, saboda ya sanya an yi zanga-zanga a majalisar dokokin Amurka, kusan shekara uku da suka wuce.

Mr Trump zai iya tsayawa takarar shugabancin kasar a shekara mai zuwa, sai dai hukuncin zai kara haifar masa da sarkakiya.

Masu yi masa yakin neman zabe sun sha alwashin daukaka kara zuwa kotun kolin kasar.

Masu bashi shawara sun soki hukuncin, sun ce "mai rauni ne matuka".

Hukuncin na magana ne kadai a kan zaben fidda gwanin da za a yi a jihar a ranar 5 ga watan Maris din shekara mai zuwa, lokacin da jam'iyyar Republican za ta zabi wanda zai tsaya mata takarar shugabancin kasa.

Sai dai hakan zai shafi babban zaben da za a yi a watan Nuwambar shekarar ta 2024.

Wannan ne karon farko da aka yi amfani da sashe na uku na kudin tsarin mulkin da aka yiwa gyaran fuska na 14, wajen hana dan takarar shugaban kasa tsayawa.

Hukuncin na ranar Talata wadda ba za a yi aiki da shi ba tukuna har sai an daukaka kara a watan gobe ya shafi jihar ta Colorado ne kadai.

Ire-iren wadandan yukuri na cire tsohon shugaban kasar a sahun 'yan takara a jihohin New Hampshire da Minnesota da kuma Michigan ba su yi narasa ba.

Hukuncin da alkalan suka rubuta ya ce: "Cimma wannan matsayi ba abu ne da ya zo mana da sauki ba. Muna sane da irin girma da nauyin tambayoyin da za mu fuskanta.

"Haka zalika muna sane da girman rantsuwar da muka yi na yin aiki da doka ba sani ba sabo kuma ba tare da mun bar ra'ayoyin jama'a sun yi tasiri a kanmu ba, kan hukuncin da ya zama dole mu cimma.

Hukuncin dai ya warware hukuncin da wani alkali ya bayar a Colorado tun da fari, wanda ya ce sashen kundin tsarin mulkin bai shafi dan takarar shugaban kasa ba, domin bai fito karara ya fadi hakan ba.

Alkalin karamar kotun ne kuma ya samu Mr. Trump da hannu a boren da aka yi a majalisar dokokin kasar ta Capitol.

Masu goyon bayansa sun farwa majalisar a ranar 6 ga watan January, 2021, yayin da 'yan majalisar ke tabbatar da nasarar lashe zaben da shugaba Biden ya yi.

Hukuncin Kotun kolin ta Colorado ba zai fara aiki ba sai ranar 4 ga watan Janairun 2024.

Kuma wannan ranar ita ce jajiberin wa'adin da aka sanya wa jihar na wallafa kuri'un da za a kada na zaben fidda gwanin 'yan takarar shugabancin kasar.

Steven Cheung, shi ne kakakin yakin neman zaben tsohon shugaban kasar, kuma ya bayyana hukuncin da cewa "mai rauni ne matuka" sannan ya yi wa alkalan wankin babban bargo, wadanda gwamnonin jam'iyyar Democrat ne suka nada su.

"Shugabannin Democrat a jihar sun shiga yanayi na tsoro saboda rinjaye da goyon bayan da shugaba Trump ke samu a kuri'ar jin ra'ayin jama'a" Mr Cheung ya bayyana a wata sanarwa.

Mr. Cheung ya kara da cewa lauyoyin da ke wakiltar Mr. Trump "za su gaggauta daukaka kara" zuwa kotun kolin kasar, inda masu ra'ayin 'yan mazan jiya ke da rinjaye na kashi shida bisa uku.

Sai dai masu goyon bayan shugaba Biden ya sake tsayawa takara, sun ki yarda su yi magana kan hukuncin kotun kolin Colorado.

Sai dai wani babban kusa da ke da alaka da kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar Democrat ya shaida wa kafar watsa labarai ta CBS cewa, hukuncin zai taimakawa 'yan jam'iyyar ta Democrat wajen karfafa matsayinsu na cewa abin da ya faru a majalisar ta Capitol, yukuri ne na yi wa hukumomi bore.