Ya za a yi da Sallar Idi idan ta faɗo ranar Juma'a?
Ya za a yi da Sallar Idi idan ta faɗo ranar Juma'a?
An wallafa
Ganin cewa Ƙaramar Sallah a bana za ta iya faɗowa ranar Juma'a, addinin Musulunci tuni ya yi tanadi game da haɗa waɗannan ibadun biyu.
Hukumomi a Saudiyya tuni suka ba da rahoton cewa an ga watan Shawwal a can, yayin da sauran ƙasashe ke ci gaba da duban watan sallar.
BBC ta tattauna da wasu malaman addinin Musulunci biyu, Sheikh Ahmad Gumi da Sheikh Halliru Maraya domin jin fatawoyin malamai a kan haka.



