Abin da ke jefa ‘yan mata cikin matsalar shaye-shaye

Abin da ke jefa ‘yan mata cikin matsalar shaye-shaye
An wallafa

Wani bincike wanda shi ne irinsa na farko da aka gudanar kan shan miyagun kwayoyi a Najeriya, ya nuna cewa mata 2.6 miliyan ne ke shan wiwi a kasar.

Kimanin mutane miliyan 10.6 ne binciken ya gano suna shan wiwi a shekarar 2017 a kasar, inda kowane mutum hudu da ke sha daya daga cikinsu mata ne.

Inda ‘yan mata matasa suka kasance cikin miliyoyin matan da ke shan wiwi da sauran miyagun kwayoyi a kasar.

Haka kuma binciken ya nuna wasu karin na’ukan miyagun kwayoyi bakwai da ake tu’ammali da su a kasar.

Hukumar lafiya ta duniya, reshen Afrika ta ce wiwi shi ne ke kan gaba a jerin miyagun kwayoyin da aka fi tu’ammali da su a duniya. Inda kimanin mutane miliyan 129 zuwa miliyan 190 ne hukumar ta bayar da kiyasin suna tu’ammali da wiwi a duniya.

Yayin da a Afrika, matsalar ta fi kamari a yammacin Afrika da kuma tsakiyar nahiyar.

Jinsi da shekaru da kaurar mutane daga yankunan karkara zuwa birane na daga cikin dalilan da ke jefa mutane fara tu’ammali da miyagun kwayoyi.

WHO reshen Afrikan ta kara da cewa, magungunan nau’oin Amphetamine wato ATS da suka hada da ecstasy da methamphetamine da ake hadawa a dakunan gwaje-gwaje su ne miyagun kwayoyin kashi na biyu da aka fi tu’ammali da su a nahiyar.

Hukumar ta yi nuni da cewa babban mummunan tasirin da tu’ammali da miyagun kwayoyi ke yi shi ne illa ga lafiyar masu shansu.

Bugu da kari hakan na janyo wani babban nauyi na kashe kudade a bangaren iyalansu da daidakun mutane da kuma al’umma baki daya.