Lafiya Zinariya: Dalilan da suka sa mata suka fi maza saurin tsufa 07/12/2024

Lafiya Zinariya: Dalilan da suka sa mata suka fi maza saurin tsufa 07/12/2024
An wallafa

Masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana wasu dalilai da suka ce suna sanya mata tsufa da wuri fiye da maza.

Wasu daga cikin dalilan sun haɗa da bambancin halitta, inda mata ke hayayyafa da ɗawainiyar yara.

Kasancewar mata na da mahaifa, su kan samu wasu cututtukan da maza ba sa samu.

Yawan al'ummar duniya masu shekaru 80 zuwa sama za su ninka kusan sau uku, inda za su kai miliyan 426 a tsakanin shekarar 2020 zuwa 2050, a cewar hukumar lafiya ta duniya.

Inda ta ƙara da cewa ƙaruwar shekaru a duniya zai yi tasiri ne idan yana tafe tare da lafiya.

Latsa makunnin da ke sama domin jin ƙarin bayani kan hanyoyin da za a iya bi wajen kyautata rayuwar dattawa daga bakin Dr. Ruƙayya Ali Munir.