Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Burin China a yaƙin Isra'ila da Hamas
Yayin da yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas ke tsananta, ƙasar China ta yi yunƙurin shiga tsakani, sai dai akwai iyaka a rawar da ƙasar za ta iya takawa don tsagaita yaƙin.
A ƙarshen mako babban jami'in diplomasiyar China, Wang Yi, ya tattauna batun rikicin da jami'ai a Amurka, yayin da ake fargabar yaƙin zai iya shafar yankin Gabas ta Tsakiya.
Amurka ta alƙawarta yin aiki tare da China a ƙoƙarinta na kawo sasanci a yaƙin.
Mista Wang ya kuma zanta da takwarorinsa na Isra'ila da Falasɗinawa bayan da jakadan China na musamman a yankin Gabas ta Tsakiya Zhai Jun ya ziyarci yankin domin tattaunawa da shugabannin Larabawa.
Tattaunawar ta kasance ɗaya daga cikin manyan kiraye-kirayen tsagaita wuta a tarukan MDD.
Ana sa ran China za ta yi amfani da alaƙarta da Iran - wadda ke goyon bayan ƙungiyar Hamas a Gaza da ƙungiyar Hezbollah a Lebanon - domin warware rikicin.
Jami'an Amurka sun buƙaci Mista Wang da Iran su "saita al'amura" , kamar yadda Jaridar Financial Times ta ruwato.
China ta kasance babbar abokiyar cinikayyar kasuwanci ga mafi yawan ƙasashen Gabas ta Tsakiya, sannan a farkon wannan shekara ƙasar, ta yi koƙarin daidaita tsakanin Iran da Saudiyya waɗanda suka jima ba su ga-maciji da juna.
Tehran ta ce a ''shirye take ta ƙarfafa ƙawancenta'' domin sasanta rikicin Gaza.
Yayin da gwamnatin China ke da alaƙa da duka ɓangarorin da ke faɗa da junan, za su iya ɗaukarta a matsayin mai gaskiya a ƙoƙarin da take yi don shiga tsakani a rikicin, kamar yadda Dawn Murphy, wata ƙwararriya kan harkokin ƙasashen waje a ma'aikatar tsaron Amurka ta bayyana.
"Ita kanta China, na da kyakkyawar alaƙa da Falasɗinawa da Turkiya da Iran da sauran ƙasashen Larabawa", in ji ta.
"Ta hanyar yin aiki da Amurka - wadda ke da dangantaka mai ƙarfi da isra'ila - za su iya kawo duka ɓangarorin da ke rikici kan teburin sulhu", in ji Murphy.
Amma wasu masu sharhi na ganin cewa China ba ta da ƙarfi a siyasar yankin Gabas ta Tsakiya.
"China ba ta da ƙarfin faɗa-a-ji a wannan rikici. Game da yin magana da mutanen da ke yankin, babu wanda zai yi tsammanin China za ta iya kawo ƙarshen yaƙin," in ji Jonathan Fulton, wani ƙwarraren masanin dangantakar China da ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya.
Sanarwar farko da China ta fitar game da yaƙin, ta hasala Isra'la, wadda ta bayyana "matsanancin fushinta", saboda China ba ta yi alla-wadai da hare-haren Hamas ba, sannan a gefe guda ba ta ce Isra'ila na da damar kare kanta ba.
Mayaƙan Hamas sun ƙaddamar da hare-hare daga Gaza kan Isra'ila ranar 7 ga watan Octoba, inda suka kashe fiye da mutum 1,400 tare da yin garkuwa da aƙalla mutum 139.
Tun daga lokacin ne Isra'ila ke ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya a Gaza, inda ta kashe Falasɗinawa fiye da kusan sama da 9,500, kamar yadda ma'aikatar lafiyar da Hamas ke jagoranta ta bayyana.
A yanzu kuma Isra'ila ta tura ƙarin dakaru da tankokin yaƙi zuwa yankin.
Bayan bayyana fushi kan sanarwarta ta farko, daga baya Mista Wang ya faɗa wa Isra'ila cewa "kowace ƙasa na da damar kare ƙanta", sai dai ya faɗa a wani wuri cewa matakin da isra'ila ta ɗauka ya "zarta da'irar kare kai".
China na cikin tsaka-mai-wuya wajen yin adalci ga kowane ɓangare, saboda ta jima tana nuna tausayinta a fili ga Falasɗinawa.
Lamarin ya faro ne tun lokacin da jagoran jam'iyar kwamunisanci Mao Zedong, wanda ta aika wa Falasɗinawa da makamai domin nuna goyon abin da suka kira yunƙurin "fafutikar neman 'yancin kai' a faɗin duniya.
A lokacin, Mao ya ma kwatanta Isra'ila da Taiwan - waɗanda duka ke samun goyon bayan Amurka - a matsayin sansanonin ƙasashen Yamma.
Gomman shekaru bayan nan, China ta buɗe ƙofar daidaitawa da isra'ila ta hanyar ƙulla ƙawancen kasuwanci da ita, inda a yanzu ƙasashen biyu ke da ƙawancen kasuwanci na biliyoyin dala.
To amma China ta bayyana ƙarara cewa za ta ci gabata da tallafa wa Falasɗinawa.
A jawabinsu kan rikicin baya-bayan nan, jami'an China ciki har da Shugaba Xi Jinping sun jaddada buƙatar samar da ƙasar Falasɗinawa mai zaman kanta.
Babbar illar da hakan ya janyo ita ce haifar da ƙyamar Isra'ila a shafukan intanet, musamman daga 'yan kishin ƙasa masu amfani da shafukan sada zumuntar China.
Wasu shafukan sada zumunta a china sun kwatanta abin da Isra'ila ke yi da abin da Nazi ta yi, ta hanyar zargin su da kai hare-haren kisan ƙare-dangi kan Falasdinawa, lamarin da ya haifar da suka daga ofishin jakadancin Jamus a Beijing.
Daɓa wa wani mutum ma'aikacin ofishin jakadancin Isar'ila a Beijing wuƙa ya ƙara ta'azzara lamura.
Duka waɗannan ba za su yi wa China daɗi ba, idan ta yi ƙoƙarin zama da gwamnatin Isra'ila.
Duk da wannan rashin tabbaci, ta yaya hakan ya shafi China?
Dalili ɗaya shi ne muradinta a tattalin arzikin yankin Gabas ta Tsakiya, wanda zai gamu da cikas idan yaƙin ya ci gaba da faɗaɗa.
A yanzu China ta dogara sosai kan man fetur da take saya daga ƙetare, kuma masu sharhi sun ƙiyasta cewa kusan rabinsa daga ƙasashen yankin Gulf take samu.
Ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya sun ci gaba da kasancewa muhimman masu taka rawa a haɓakar tatalin arzikin China.
Wani dalilin kuma shi ne rikicin ya samar wa China babbar damar bunƙasa kanta.
China ta yi amanna cewa "goyon bayan Falasdinawa zai yi daidai da muradin ƙasashen Larabawa, ƙasashen da Musulmai suka fi yawa kuma suke da yawa a kudancin duniya", in ji Dakta Murphy.
Yaƙin ya ɓarke ne a daidai lokaci da China ke ƙoƙarin nuna kanta a matsayin wadda ta fi dacewa da ƙasashe su ƙulla ƙawance da ita fiye da Amurka.
Tun farkon wannan shekara ƙasar ke ƙoƙarin bunƙasa jagorancinta ga duniya, yayin da take sukar Amurka kan abin da ta kira ƙarfa-ƙarfan" jagoranci.
A hukumace, China ta ƙi sukar Amurka kan goyon bayan Isra'ila. Amma a lokaci guda kuma, kafar yaɗa labaran ƙasar na "nuna kishin ƙasa...inda suke nuna cewa abin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya Amurka na goyon bayansa," in ji Dr Muphy.
Jaridar rundunar sojin China ta PLA Daily ta zargi Amurka da "tunzura rikicin", irin zargin da China ta yi amfani da shi wajen sukar Amurka kan taimaka wa Ukraine a yaƙin Rasha.
Daya daga cikin ra'ayoyin masu sharhi shi ne China na ƙoƙarin saɓa wa ra'ayin Amurka, saboda hakan zai sa ta rage wa kanta hamayya daga ƙasashen Yamma.
Sai dai rashin yin alla-wadai da Hamas zai iya jefa china cikin hatsarin rasa matsayi ko kimarta.
Akwai ƙalubalen da China ke fuskanta game da tabbatar da manufofinta na shekaru masu zuwa.
Daya daga ciki shi ne yadda za ta daidaita huldar diflomasiyyarta da kasashen waje da kuma abubuwan da ta aiwatar a baya.
A yayin da take nuna goyonta ga ƙasashen da Musulmai suka fi yawa, tare da rashin goyon bayan mamayar da Isra'ila ke yi wa yankunan Falasdinawa, hakan ya sa ana zargin ta da tauye 'yancin ɗan'adam tare da aikata kisan kiyashi ga Musulmai 'yan ƙabilar Uyghur marasa rinjaye, da tilasta mamaya a Tibet.
Masu sharshi na cewa wannan ba lallai ne ya zama wani abu ga ƙasashen Larabwa ba, saboda ƙarfin alaƙar da China ta gina tsakaninsu.
Babbar matsalar ita ce China na fuskantar barazanar zama babbar mai fada-a-ji, ko ma fiye, inda take ƙoƙarin amfani da rikicin Isra'ila da Hamas domin kare muradunta.
Mista Wang ya yi iƙirarin cewa China na son zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya kawai, kuma ba ta da "wani muradi kan Falasɗinawa".
Sai ƙalubalen shi ne ta yadda za ta iya gamsar da duniya gaskiyar hakan.