Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amsoshin Takardunku: Tarihin Ghali Umar Na'Abba
Amsoshin Takardunku: Tarihin Ghali Umar Na'Abba
An wallafa
A ranar Laraba 27 ga watan Okotoba, Allah ya yi wa tsohon shugaban Majalisar Wakilan Najeriya Ghali Umar Na'Abba.
Ya rasu ne a wani asibiti da ke Abuja babban birnin ƙasar, inda ya kwanta don jinya.
Ghali Na'Abba dai ya jagoranci Majalisar wakilan Najeriya ne daga shekarar 1999 zuwa 2003.
Ya yi suna sakamakon jan zaren da ya yi da tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo, wanda rahotanni suka ce ya nemi yin tazarce a ƙarshen wa'adin mulkinsa na biyu.