Nijar na son bayani kan yadda aka sayar da dutsen Mars ɗinta a Amurka

    • Marubuci, Damian Zane
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Jamhuriyar Nijar na neman amsa game da wani dutse na musamman wanda ya faɗo daga duniyar Mars wanda kuma shi ne mafi girma da ya faɗo, kuma aka sayar da shi a birnin New York na Amurka kan dala miliyan 4.3.

Wani masanin tsirrai da duwatsu, Farfesa Paul Sereno, wanda ke da alaƙa ta musamman da Nijar, ya nuna fushinsa kan yadda aka sayar da wannan dutsen da aka gano shekaru biyu da suka wuce a Nijar ga wani da ba a bayyana ko shi waye ba.

Wannan dutse mai shekaru miliyoyi da yawa daga duniyar Mars shi ne mafi girma da aka samu a duniyarmu ta Earth kuma an sayar da shi a gidan siyar da kayan tarihi na Sotheby's, amma ba a sani ba ko wani ɓangare na kuɗin ya shiga hannun jamhuriyar ta Nijar.

Dutsen sararin samaniya kamar wannan yana da daraja sosai, wasu suna ɗaukar su a matsayin kayan addini ko abubuwan ban sha'awa, yayin da wasu ke binciken su don kimiyya.

Kasuwancin irin waɗannan duwatsun na kama da kasuwar kayan fasaha, inda ƙima da ƙarancin samuwarsu ke ƙara farashinsu.

A farko, mutane sun yi mamakin ganin wannan dutsen Mars ɗin na musamman lokacin da aka bayyana shi ga bainar jama'a, saboda daga cikin dubunnan duwatsun da aka gano, ƙasa da 400 ne aka tabbatar sun fito daga duniyar Mars.

Hotunan dutsen wanda ake kira NWA 16788 kuma mai nauyi 54lb (ko kuma kilogiram 245) sun nuna yana haskakawa da launin azurfa da ja, wanda ya ƙara wa mutane sha'awa.

Amma daga baya, mutane suka fara tambayar yadda aka fitar da wannan dutse daga Nijar kuma aka siyar da shi a kasuwa.

Gwamnatin Nijar ta nuna damuwa game da yadda aka fitar da dutsen, inda take fargabar yiwuwar fitar da shi ta haramtacciyar hanya.

Sotheby dai ta musanta wannan zargi sosai, tana cewa an bi duk hanyoyin da suka dace wajen fitar da dutsen, amma yanzu gwamnatin Nijar ta fara bincike game da yadda aka gano wannan dutse da yadda aka sayar da shi.

An gano dutsen Mars ɗin a hamadar Sahara a yankin Agadez na Nijar a ranar 16 ga Nuwamban 2023, daga wani mafaraucin dutse wanda ba a bayyana sunansa ba.

Dutse irin wannan na iya faɗowa ko'ina a duniya, amma saboda yanayin Sahara da dacewar wurin wajen adana abubuwa da kuma rashin tsangwama daga mutane, ana samun irin waɗannan duwatsu na musamman da yawa a wannan yanki.

Mutane suna shiga cikin wannan yanki mai tsananin zafi domin neman irin waɗannan duwatsu saboda su sayar.

Rahoto daga wani binciken ƙwararru na Italiya ya bayyana cewa al'ummar garin ta sayar da wannan dutse ga wani dillali wanda daga baya ya kai shi wani gidan kayan tarihi a birnin Arezzo na Italiya.

Ƙungiyar masana kimiyya ƙarkashin jagorancin farfesa Giovanni Pratesi daga jami'ar ta yi nazari kan dutsen Mars ɗin don gano asalinsa da yadda aka samar da shi.

An kuma nuna dutsen a fili a Italiya a shekarar da ta gabata, har ma da birnin Roma.

Daga baya, aka nuna shi a New York a watan da ya gabata, sai dai an cire wasu ɓangori guda biyu daga cikin dusten wanda aka bar su a Italiya don ci gaba da bincike.

Wakilin Sotheby ya kara da cewa suna sane da rahotannin binciken da Nijar ke yi game da fitar da dutsen, kuma suna duba bayanan da ke akwai don amsa tambayoyin da aka yi.

Farfesa Sereno, wanda ya kafa ƙungiyar NigerHeritage shekaru goma da suka wuce, ya yi imanin cewa an karya dokokin Nijar wajen fitar da wannan dutse.

Farfesa Paul Sereno daga Jami'ar Chicago, wanda ya shafe shekaru yana gano ƙasusuwan dodonnin da suka mutu a hamadar Sahara, yana fafutukar a mayar wa da Nijar duk wani kayan tarihi na ƙasar, har da duk wani abu da ya faɗo daga sararin samaniya.

Ana shirin gina wani babban gidan tarihi a tsibiri a kan kogin Nijar da ke Niamey domin ajiye irin waɗannan abubuwa.

Farfesa Sereno ya ce dokar ƙasashen duniya ta hana a fitar da kayan da ke da muhimmanci ga tarihin wata ƙasa ba tare da izini ba, kuma mun wuce zamanin mulkin mallaka da hakan ke yuwuwa.

Duk da cewa yarjejeniyoyi na duniya kamar na UNESCO suna ƙoƙarin taƙaita cinikayyar irin waɗannan abubuwa, amma kuma idan ta ɓangaren irin waɗannan duwatsu da ke faɗowa daga wasu duniya zuwa duniyar Earth ne, kowace ƙasa ce ke da ikon yin tata doka.

Nijar ta kafa dokar kare kayan tarihi tun daga shekarar 1997, amma ba ta ambaci irin waɗannan duwatsun a fili ba.

A cikin bayaninta kan siyar da dutsen, gwamnatin Nijar ta ce har yanzu ba ta da doka ta musamman kan irin waɗannan duwatsu daga sararin samaniya.

Amma har yanzu ana neman amsa kan yadda aka fitar da dutse mai nauyi haka daga ƙasar ba tare da hukumomi sun lura ba.

Morocco ma ta fuskanci irin wannan matsalar, inda sama da duwatsu 1,000 aka gano a yankinta, ciki har da wani ɓangare na hamadar Sahara.

Shekaru fiye da 20 da suka wuce, marubuciya Helen Gordon ta kira abin da ya faru a can da "Tururuwa wajen neman zinariya a Sahara" saboda sassaucin doka da yanayin siyasar ƙasar.

Farfesa Hasnaa Chennaoui Aoudjehane ta shafe kusan shekaru 25 tana ƙoƙarin ajiye wasu daga cikin waɗannan duwatsu na sararin samaniya a ƙasar. Ta ce, "Wani ɓangare ne daga cikinmu, daga tarihinmu kuma daga asalinmu." Ba ta adawa da kasuwancin irin waɗannan duwatsun gaba ɗaya, amma ta taimaka wajen kafa dokoki don taƙaita hakan – amma duk da haka, ta amince cewa hakan bai dakatar da fitar da duwatsun ba.

A 2011, ta tattara wani dutse daga Mars da ya faɗo a hamada, wanda aka kira Tissint, mai nauyin kilo 7, amma yanzu kilo 0.03 ne kawai ke nan a Morocco. Ana kai sauran gidajen tarihi a duniya.

Game da batun dutsen Mars na Nijar, ta ce ba ta yi mamaki ba, domin ta daɗe tana fuskantar haka.