Man Utd na zawarcin Raphinha, Osimhen zai koma Ingila

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United ta gabatar da tayin yuro miliyan 70 (£58.9m) kan ɗan wasan gaba a Brazil Raphinha, mai shekara 28, daga Barcelona. (Fichajes.net)

Dole Manchester City ta biya akalla fam miliyan 70 idan tana son ɗan wasan tsakiya Eduardo Camavinga, mai shekara 22, ya bar Real Madrid. (Football Insider)

Arsenal da Chelsea sun wuce Liverpool a farautar ɗan wasan Inter Milan da Faransa, Marcus Thuram mai shekara 27, wanda ake neman fam miliyan 71 a sharudan yarjejeniyar sayar da shi. (Football Insider, external)

Tottenham Hotspur na cikin ƙungiyoyin Firimiya da dama da ke bibbiyar ɗan wasan tsakiya a Inter Miami na Amurka, Benjamin Cremaschi mai shekara 20. (TBR Football)

AC Milan ta aike wakilai domin sa ido kan ɗan wasan baya a Burnley, Maxime Esteve mai shekara 22, amma Everton da West Ham su suma ba a bar su a baya ba a wannan farauta. (Alan Nixon via Football League World)

Arsenal na duba yiwuwar saye ɗan wasan Ajax, Jorrel Hato mai shekara 19, yayinda Myles Lewis-Skelly ke cikin rashin tabbas. (TBR Football)

Newcastle na son ta cigaba da rike ɗan wasan Sweden, Alexander Isak amma hakan ba zai hanata ci gaba da sanya ido kan wasu 'yan wasan ba, ciki har da matashin nan na Ipswich, Liam Delap mai shekara 22, da mai taka leda a Sporting, Viktor Gyokeres, mai shekara 26, domin maye gurbinsa idan ya yanke hukunci tafiya ganin Liverpool ta bude wuta. (Teamtalk, external)

Ɗan wasan Amurka kuma tsohon ɗan wasan gaba a Chelsea, Christian Pulisic mai shekara 26, na tattauna sabon kwantiragi da AC Milan. (ESPN, external)

Da alama ɗan wasan gaba a Napoli, Victor Osimhen mai shekara 26, da ke zaman aro a Galatasaray, zai koma buga Firimiya a sabuwar kaka, a cewar abokin aikinsa daga Najeriya, William Troost-Ekong. (Talksport, external)