Ni da wariyar launin fata mun yi hannun riga - Mourinho

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Fenerbahce Jose Mourinho ya ce shi "sun yi hannun riga da wariyar launin fata" bayan an zarge shi da yin kalaman wariya ka 'yanwasan Galatasaray.

Galatasaray ta ce za ta "kai ƙara kotu" game da kalaman na Mourinho saboda ya yi "kalaman wariya" bayan karawar da suka tashi 0-0 a tsakaninsu ranar 24 ga watan Fabrairu.

"Ba su yi dabara ba a suka ta da suka yi, saboda ba su san tarihina ba," kamar yadda ya shaida wa Sky Sports.

"Ba su san alaƙata da Afirka ba, da 'yan Afirka, da 'yanwasan Afirka, da ƙungiyoyin agaji na Afirka.

"Maimakon su samu nasara a kaina, ina ganin abin ya koma kansu."

Bayan wasan hamayyar na birnin Istanbul, Mourinho ya ce 'yanwasan Galatasaray masu masaukin baƙi "sun yi ta tsalle kamar birai" a lokacin wasan, inda Fenerbahce daga baya ta ce "an sauya wa kalaman Mourinho manufa".

Mourinho mai shekara 64, shi ma ya kia ƙarar Galatasaray kotu yana neman a biya shi diyyar 1,907,000 na Lira kuɗin Turkiyya (fam 41,000) sakamakon ɓata masa suna.

"Kowa ya san ni wane ne. Kowa ya san matsalolina, amma wannan ba shi cikin matsalolina. Akasin haka ne ma!" in ji shi.

"Abu mafi muhimmanci dai shi ne ni na san wane ne ni, kuma suka ta da sunan wariyar launin fata zaɓi ne maras kyau."

Tsohon ɗanwasan gaba na Ivory Coast Didier Drogba, da ɗanwasan tsakiya na Ghana Michael Essien - waɗanda suka taka leda a ƙarƙashin Mourinho - sun kare tsohon kocin nasu.