Kwara United ta samu maki uku a kan Kano Pillars

Asalin hoton, NPFL
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1
Kwara United ta yi nasara a kan Kano Pillars da ci 2-0 a wasan mako na 28 a gasar Premier ta Najeriya ranar Lahadi.
Wasiu Alalade ne ya fara cin ƙwallo a minti na 20 a bugun fenariti, sannan Wasiu Jimoh ya kara na biyu a zagaye na biyu.
Da wannan sakamakon Kano Pillars ta yi kasa zuwa mataki na shidan teburi da maki 42, bayan cin wasa 12 da canjaras shida aka doke ta karawa ta 10.
Ita kuwa Kwara United mai maki 39 tana ta 11 a teburin babbar gasar tamaula ta Najeriya.
Sakamakon wasannin da aka buga ranar Lahadi:
- Kwara Utd 2-0 Kano Pillars
- Nasarawa Utd 1-1 Sunshine Stars
- Enyimba 1-0 El-Kanemi
- Rangers 1-1 Akwa Utd
- Plateau Utd 1-0 Abia Warriors
- Heartland 1-1 Bayelsa United
Sakamakon wasannin ranar Asabar:
- Bendel Insurance 2-1 Remo Stars
- Lobi Stars 0-1 Ikorodu City
Sakamakon wasan ranar Alhamis:
- Katsina United 1-0 Shooting Stars Sports






