Lafiya Zinariya: Da gaske ana ɗaukar amosani ta mataji ko kibiyar kitso?

Lafiya Zinariya: Da gaske ana ɗaukar amosani ta mataji ko kibiyar kitso?
An wallafa

Amosari wani ciwo ne da ke samun fata saboda jiki baya son wata kwayar cutar da ake kira Fungus a likitance.

Don haka ba ƙazanta ba ce ke janyo shi, a cewar masana.

Cutar amosari da musamman ya ke fitowa a fatar kai, tana kuma fitowa a wasu sassan jiki kamar fuska da hammata da ƙasan nono ko a gaban mutum.

Sai dai ba a ɗaukarta sakamakon amfani da kibiya/masulla ko mataji na wadda ke fama da cutar.

A cewar likitoci cuta ce da ke samun jarirai, babba da yaro, mata da maza.

Haka zalika cuta ce da kan ɗauki dogon lokaci kafin ta warke.

Sai dai mace ko mai fama da amosari kan iya ɗaukar matakan magance shi a gida ta hanyar amfani da mayukan wanke kai da ke kashe amosari. Haka kuma amfani da mayukan kisto da ke rage ƙaiƙayi da raɗaɗin da amosari ke janyowa.

Amma idan ya yi ƙamari sai a je asibiti wurin likitan fata, wanda zai bayar da magani da kuma sauran shawarwarin yadda mutum zai rabu da amosarin.