Jam'iyyun hamayyar Najeriya na martani kan dakatar da Sanata Ningi

An wallafa

A Najeriya, jam'iyyun hamayyar kasar sun yi Allah-wadarai da matakin da majalisar dattawa ta dauka na dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon wata uku, bayan da ya yi wasu kalamai da ke nuna an cusa wasu kudi naira kusan tiriliyan hudu, wadanda ba a san inda aka nufa da su a kasafin kudin kasar na bana ba.

Jam'iyyun hamayyar suna ganin kamata ya yi a fara da gudanar da bincike kan batun cushen kudin, don a tabbatar da gaskiya ko akasin zargin, kafin a dauki matakin dakatar da dan majalisar.

Matakin dakatar da Sanata Abdul Ningi, na tsawon wata uku da majalisar dattawan Najeriyar ta dauka, na ci gaba da shan suka, har ma bakin wasu jam'iyyun hamayya na kasar ya zo daya, wajen yin tir da lamarin.

Jam'iyyarsa ta PDP, ta bayyana matakin a matsayin wani yunkuri na hana gudanar da bincike, da yin balulluba, da kuma yi wa 'yan Najeriya wuji-wuji ina gabas kan batun da ya bankado.

Jam'iyyar ta ce tana goyon bayan Sanatan nata game da matakin da ya dauka na yayata badakalar da yake zargin an yi, a cewar Ibrahim AbdulLahi, mukaddashin jami'in hulda da jama'a na kasa na jam'iyyar.

"Ya yi abin da ya dace wanda muke goyon baya a matsayinmu na jam'iyya, kuma na tabbata duk ƴan Najeriya na goyon bayan wannan ƙorafi da aka yi saboda irin wannan zaluncin ne ya durkusar da Najeriya," in ji Ibrahim AbdulLahi.

A nata ɓangaren, jam'iyyar PRP, na ganin akwai lauje cikin nadi, game da matakin dakatar da dan majalisar dattawan.

Abdullahi Ahmad Wakili, wani tsohon ɗan takarar kujerar sanata na jam'iyyar a jihar Kaduna, ya ce, "maimakon majalisar ta kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar lamarin, sai kawai aka dakatar da shi na wata uku, saboda haka mu a matsayin jam'iyarmu ba mu yarda da hakan ba, kuma muna kira ga duk hukumomin bincike da su gudanar da bincike."

Jam'iyar LP ita ma ta nuna damuwarta kan matakin, inda kakakin jam'iyyar, Dakta Yunusa Salisu Tanko, ya ce suna tare da bayanin da Sanata Ningi ya yi kuma suna kira da a yi bincike kan bataun kasafin kudin.

Lamarin dai na ci gaba da daukar hankali tare da haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya, kuma ana nan an zura ido a ga yadda a karshe lamarin zai kaya.