Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mini Hanya: Tare da Dr Jamila Aliyu Dikko kan ciwon kai
Ciwon kai, larura ce ga ɗumbin mutane a duniya, wasu ma ba tare da sun san taƙamaimai nau'in da ke damun su ba.
Wasu larurorin ƙwaƙwalwa, a cewar ƙwararru na farawa ne da sigar ciwon kai.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce rashin ilmin ciwon kai hatta a tsakanin jami'an lafiya, wani babban tarnaƙi ne wajen ganowa da magance shi.
Jama'a dai ba sa ɗaukan ciwon kai a matsayin wata babbar larura tun da ciwo ne da ba ya kisa kuma ba a yaɗa shi, amma yana iya hana sukuni, ya hana aiki ko zuwa makaranta, kai yana ma iya zama alama ta wani babban ciwo mai buƙatar ɗaukin likita cikin gaggawa.
A filinmu na Gane Mini Hanya, Madina Ɗahiru Maishanu ta tattauna da wata likitar ciwon kai, Dr. Jamila Aliyu Dikko kuma ta fara da tambayarta ko me ya sa ta zaɓi mayar da hankali kan fannin ciwon kai?