Gane Mini Hanya tare da sarkin Dutse

Gane Mini Hanya tare da sarkin Dutse
An wallafa

A ranar biyar ga watan Fabrairu ne aka naɗa Alhaji Hamim Nuhu Sunusi a matsayin sabon sarkin Dutse bayan rasuwar mahaifinsa Dakta Nuhu Muhammadu Sunusi.

A tattaunawarsa da BBC watannin uku bayan hawansa kan karagar mulkin masarautar, sabon sarkin ya ce zai ƙara himma wajen haɗa kan al'umma da zaburar da matasa wajen neman na kansu.

Sabon sarkin ya ce a lokacin da aka naɗa shi sarki ya ji daɗi, domin kuwa a cewarsa burin kowannen ɗan sarki, shi ne ya zama sarki.

Ya ce yana godiya da fatan alkairi da waɗanda suke ba shi goyon bayan, wajen gudanar da al'amura